Wasanni

Wasanni

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

00:00
00:00

Riassunto dell'episodio

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya maida hankali ne kan nasarar lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekaru 17 da tawagar Flamingos ta Najeriya ta yi, bayan da ta lallasa takwararta ta Japan a wasan ƙarshe da ci 2-1. Tuni dai shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje ƴan matan da kyautar naira miliyan Ɗari-ɗari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............

Episodi

688-

Tagomashin da tawagar Flamingos ta samu bayan lashe kofin duniya

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya maida hankali ne kan nasarar lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekaru 17 da tawagar Flamingos ta Najeriya ta yi, bayan da ta lallasa takwararta ta Japan a wasan ƙarshe da ci 2-1. Tuni dai shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje ƴan matan da kyautar naira miliyan Ɗari-ɗari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............

16 Nov 2026
687-

Bamuji ɗaɗin irin rabuwar da aka yi tsakanin Ronaldo da Portugal ba - Ra'ayoyi

Shirin na duniyar wasanni a wannan lokaci yayi duba ne game da bankwana da tawagar Portugal da Ronaldo yayi. A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa, lamarin da ke kawo ƙarshen shekaru fiye da 20 da ya shafe yana wakiltar ƙasar shi a matakin ƙwallon ƙafar duniya. Cikin saƙon na Ronaldo, ya ce bayan nutsuwa cikin tsananki ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen wakiltar ƙasar shi kodayake ya ce Portugal za ta ci gaba da kasancewa a zuciyar shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............

09 Nov 2026
686-

Sharhi akan kyautar Ballon d'Or ta 2026 wadda Harry Kane ya lashe

Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........

02 Nov 2026
685-

Sharhi kan yadda ta kaya a wasan El-Clasico da aka yi a ƙarshen mako

Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya maida hankali kan wasan El-Clasico da aka yi tsakanin Barcelona da Real Madrid. Shi dai wasa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi ba wai wasa bane na gama gari, domin yanada ɗinbin tarihi ganin cewa an faro shine a shekarar 1902, kuma wancan lokacin Barcelona ce ta fara samun nasara kan Madrid da ci 3-1. Sai dai a wasan na daren jiya Lahadi Madrid ce ta samu nasara da ci 2-1. Sakamakon wannan wasa ya bada mamaki matuƙa, domin dai an yi tunanin Barcelona za ta yi wa Madrid Kukkunge ne, kasancewar tana gida tare da goyon bayan mutane dubu 62,650 da suka taru a filin wasan Spotify Camp Nou, domin ganin yadda zata kaya. Haka nan ƙungiyar ta kwashe sama da shekara guda ba tare da tayi rashin nasara a filin ba, domin rashin nasara ta ƙarshe da tayi a nan ita ce a hannun Villarreal a ranar 18 ga watan Mayun shekarar bara, gashi kuma tayi nasara a wasanni 6 cikin 7 na haɗuwarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............

26 Ott 2026
684-

Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros

Shirin 'Duniya Wasanni' a wanan mako tare da Khamis Saleh zai dubu ne kan nasarar da tawagar Super Falcons ta samu kan Comoros, inda a makon da ya gabata ne aka kammala wasa na biyu na zagaye na biyu na neman zuwa gasar Olympics da aka yi tsakanin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Coromos. An dai buga dukkanin wasanni biyu ne a filin wasa na Remon Star da ke garin Ikenne na jihar Ogun, inda a wasan farko Super Falcons ta samu nasara da ci 2 da nemam sannan a wasa na biyu aka tashi 5 da nema, a jumlace gida da waje Najeriya ta jefa kwallaye biyar da nema a ragar Comoros.

19 Ott 2026